An kama matasa da suka taushe dan shekara 17 suka sadu da shi a bayansa kamar mace


Rundunar yansandan jihar Katsina ta kama mutum biyar bisa zargin aikata Luwadi da wani yaro dan shekara 17 a lokutta daban daban.

Kakakin hukumar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya ce wadanda aka kama sun yi lalata da saurayin ala tilas bayan sun nuna masa bindiga.

Ya ce rundunar yansandan jihar Katsina ta yi nassarar cafke wasu mutane bayan ta fasa gungunsu ranar 27/07/2021wadanda suka taushe wani yaro mai shekara 17 suka aikata lalata da shi da karfin tsiya.

Wadanda aka kama sun hada da Ibrahim Amadu, 42, wanda ke zaune a sabuwr Unguwa Quarters, Saminu Abdullahi, 25, Wanda ke zaune a Farin Yaro Quarters, Jamilu Ibrahim, 50, da ke zaune a Farin Yaro Quarter, Bashir Lawal, 30, na Gangaren Tudun Yanlihida Quarters, da kuma  Mohammed Sani, 30, Wanda ke Salauwa Quarters, dukkansu a cikin garin Katsina.

Yaron da aka ci zarafinsa ya ce wani mai suna Ibrahim Amadu ne ya kai shi wani waje a cikin birnin Katsina, ya daure hannayensa, ya kuma sadu da shi a bayansa.

Ya ce akwai wasu karin mutum 6 da suka aikata masa irin wannan aiki a lokutta daban daban.

Yansanda na ci gaba da gudanar da bincike.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari