Babbar magana: Wata gawa ta tashi lokacin da ake kokarin kaita Kabari domin bizinewa (Bidiyo)


Wani abin mamaki ya faru bayan wata gawa ta fara numfashi bayan an kammala shirin zuwa domin a binneta.

Yayin da aka bude akwatin gawa domin yanuwa da abokan arziki su sa mata albarkan karshe kafin a je a bizine ta. Sai aka kula tana numfashi. Lamari da ya ba jama'a mamaki.

Wannan lamari ya faru ne a birnin Hermel da ke Arewacin Baalbek-Hermel a kasar Lebanon.

Daga bisani an ga jama'a na kokarin ceto numfashin gawar bayan ta tashi ta hanyar danna kirjinsa .

An kira motar Asibiti ta tafi da mutumin domin samun kulawan Likita. Inda Likitoci suka tabbatar cewa wannan mutum yana raye. Sai dai sun ki yin bayani kan yadda aka yi kuskuren saka shi cikin rijistan matattu.

Kalli bidiyo a kasa:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN