Zulum ya dakatar da ayyukan ƙungiyar ACTED da ake zargin tana koya wa mutane harbin bindiga


Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin dakatar da ACTED, wata ƙungiyar agaji ta Faransa mai zaman kanta da ake zargin tana bayar da horon harbin bindiga a wani otal a Maiduguri.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ranar Asabar ta ce ƙungiyar na gudanar da atisayen koya wa mutane harbi.

Gwamnatin Borno ta ce mutanen unguwar da ke kusa da otal ɗin ne suka bayar da rahoton cewa suna jin ƙarar harbin bindiga.

"Kuma bayan sanar da rundunar ƴan sanda da suka gano ginin otal ɗin, an samu ƙananan bindigogi na koyon harbi guda uku, mutum biyu da ake ba horo, dukkaninsu ƴan Najeriya suna hannun ƴan sanda ana bincike," in ji sanarwar.

Bindigar da ake koya wa mutane harbi
ASALIN HOTON,BORNO GOV
Bayanan hoto,
Bindigogin koyon harbi da gwamnatin Borno ta ce ƙungiyar na amfani da su

Babagana Zulum: Gwamnan Borno ya ce ba ya tsoron mutuwa
Boko Haram: 'Yan gudun hijira na shiga kungiyar - Gwamna Zulum
Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da ƴan sanda suka ƙaddamar da bincike, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin rufe otal din tare da dakatar da ACTED daga duk wani aikin jin ƙai a jiharsa ta Borno.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari