Yan bindiga sun harbe dan majalisar dokokin jihar Zamfara Mohammed Ahmed har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce yan bindigan sun kashe Ahmed ne a kan hanyar Sheme zuwa Funtua, wani gari da ke kan iyakar jihar Zamfara da Katsina.
Zamfara da Katsina, jihohin da ke makwabtaka da juna a Arewa maso Yamma na cikin wuraren da yan bindiga suka addaba da hare-hare.
A halin yanzu ba a game bayyana cikaken yadda dan majalisar ya rasu ba amma Saidu Anka, magatakarda a Majalisar dokokin jihar Zamfara ya tabbatar da lamarin a cewar Daily Trust.
An kashe Ahmed ne jim kadan bayan manyan yan siyasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) tare da Gwamna Bello Matawalle.
Ku saurari karin bayani ...
Source: Legit