Hotuna: Yansanda sun tarwatsa masu zanga zangar June 12 a yankin Gudu da ke Abuja


Jami'an yansanda sun dakile zanga zangan 12 ga watan Yuni da wasu matasa suka yi ranar Asabar  a yankin Gudu da ke Birnin tarayya Abuja kamar yadda Jaridar PUNCH ta ruwaito.

Jaridar ta ce matasan sun fara zanga zangar da sanyin safiyar ranar Asabar da misalin karfe 8, inda suke nuna bacin ransu dangane da halin da kasa ke ciki a cewar rahotun Jaridar.

Masu zanga zangar da ke ta waka suna cewa "Dole BUHARI ya tafi" da "Mun yi tur da rashin adalci" daga cikin ire iren kalamai da suka yi ta furtawa a lokacin zanga zangar, sun ranta a na kare lokacin da yansanda suka fara harba barkonon tsohuwa.

Hatta Dan Jaridar PUNCH da ke daukan bidiyon zanga zangar kai tsaye yana watsawa a Facebook, ya tsere domin neman mafaka lokacin da yansanda suka fara harba barkonon tsohuwa a dandalin zanga zangar.



Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN