Jami'an yansanda sun dakile zanga zangan 12 ga watan Yuni da wasu matasa suka yi ranar Asabar a yankin Gudu da ke Birnin tarayya Abuja kamar yadda Jaridar PUNCH ta ruwaito.
Jaridar ta ce matasan sun fara zanga zangar da sanyin safiyar ranar Asabar da misalin karfe 8, inda suke nuna bacin ransu dangane da halin da kasa ke ciki a cewar rahotun Jaridar.
Masu zanga zangar da ke ta waka suna cewa "Dole BUHARI ya tafi" da "Mun yi tur da rashin adalci" daga cikin ire iren kalamai da suka yi ta furtawa a lokacin zanga zangar, sun ranta a na kare lokacin da yansanda suka fara harba barkonon tsohuwa.
Hatta Dan Jaridar PUNCH da ke daukan bidiyon zanga zangar kai tsaye yana watsawa a Facebook, ya tsere domin neman mafaka lokacin da yansanda suka fara harba barkonon tsohuwa a dandalin zanga zangar.
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari