Yan bindiga sun sace Jariri dan shekara uku a Duniya, duba yadda lamarin ya faru


Yan bindiga sun sace wani jariri ɗan shekara uku tare da mata 5 a Anguwar Epe, bayan sakandiren gwamnati (GSSS) Tungan Maje, Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin mai suna, Ishaku, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:23 na ranar Talata.

Ishaku ya bayyana cewa maharan sun shiga Anguwan cikin dabaru, inda suka fara harbi a sama domin su hana maƙota da jami'an tsaro kawo ɗauki.

Yace: "Yan bindigan sun shigo Anguwan daga jikin wani babban dutse dake bayan Epe, suna zuwa suka raba kansu gida-gida, kafin daga baya wasu tawagar sun kutsa cikin wani gida inda suka yi awon gaba da jariri ɗan shekara 3 da mata 5."

Ya ƙara da cewa kafin jami'an yan sanda su ƙariso yankin tuni yan bindigan sun gama aikin su, sun tafi da waɗanda suka yi niyyar sace wa.

Legit.ng hausa ta gano cewa Tungan-Maje dake kan hanyar zuwa Zuba-Gwagwalada na cigaba da fuskantar matsi daga yan bindiga.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta nemi a tura mata saƙo maimakon kiran waya, amma har yanzun ba ta turo amsar saƙon da aka tura mata ba.

Source: Legit.ng News

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN