Hukumar EFCC ta gurfanar da manyan ma'aikatan Primary Education Pension Board su biyar a gaban Kotu bisa zargin wawure N553.9m.
Hukumar Economic And Financial Crimes Commission ta wallafa a shafinta cewa wadanda ta kama sun hada da Daraktar kudi Hassana Moyi, Sakatare Abubakar Aliyu, Mataimakin Darakta Haliru Ahmed, Akantan kudi Kabiru Ahmed da Kashiya mai biyan kudi Dahiru Muhammad Isah.
EFCC ta gurfanar da ma'aikatan ne gaban babban Kotun jihar Sokoto ranar Litinin 28 ga watan Yuni bisa zargin hada baki da aikata ba daidai ba da kudade da suka kai N553.9m.
Sai dai wadanda ake tuhuma sun musanta zargi da ake masu a gaban Kotu. Sakamakon haka Lauyan masu kara H. E. Sa'ad ya bukaci Kotu ta sa rana domin fara shari'a gadan gadan.
Sai dai Lauyan da ke kare wadanda aka yi kara A.Y. Abubakar, ya gabatar da bukatar Kotu ta bayar da belin wadanda ake tuhuma da baki watau Oral Application.
Daga bisani Alkalin Kotun Jastis Muhammad ya bayar da belin wadanda aka gurfanar a kan N55m tare da mutum daya da zai tsaya masu, kuma hakan ta shafi kowane mutum daya a cikinsu.
Ya dage shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Juli 2021 domin ci gaba da shari'a.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari