Gwamnan arewa ya sallami ma'aikata 374 ya tilastawa wasu ma'aikata kimanin 380 yin ritaya, duba dalili


Gwamnatin jihar Neja ta sallami ma'aikata 374 yayin da ta tilastawa wasu ma'aikata kimanin 380 yin ritaya saboda saɓa wa dokokin jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hakanan kuma gwamnatin tana zargin waɗanda abun ya shafa da amfani da ranar haihuwa ta ƙarya lokacin da za'a ɗauke su aiki.

Gwamnatin ta yi ƙarin matakin albashi ga wasu ma'aikata kimanin 6,835 a ɓangarori daban-daban.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da shugaban hukumar kula da ma'aikatan jihar, Alhaji Shehu Yusuf Galadima, yayi wa manema labarai a Minna, ranar Talata.

Abubakar Sani Bello, Gwamnan Neja
Da ÆŠumi-ÆŠumi: Wani Gwamna Ya Kori Ma'aikata 374, Ya Tilasta Wa Wasu 380 Yin Ritaya a Jiharsa Hoto: thisdaylive.com

Yace: "Hukumar mu ta duƙufa sosai wajen tankaɗe da rairaya domin tabbatar da ingantattun ma'aikata, da kwarewar su a matsayin da aka basu, da kuma sanin makamar aiki."

"A halin yanzun mun gano wasu mutum 46 da suka saɓawa dokokin da ƙa'idojin mu ta hanyar gudanar da bincike da kuma gwaji, sannan mun sallame su."

"Daga cikin su akwai likita É—aya, da ma'aikatan fansho 31, akawuntoci 5, ma'aikatan lafiya 2 da kuma ma'aikatan ICT 4."

"Hakanan kuma, mun tilastawa wasu 380 yin ritaya saboda kama su da yin ƙarya a ranar haihuwarsu tun farkon lokacin da aka ɗauke su aiki." inji shi.

Mr. Galadima ya kara da cewa akwai wasu ma'aikata aƙalla 328 da aka sallama daga aiki bayan an shirya musu jarabawa a fannin takardun da suka gabatar lokacin da aka musu gwajin ɗaukar aiki.

Amma daga baya sai aka gano duka takardun na ƙarya ne, ba su da kwarewa a fannonin da suka gabatar.

Gwamnati ta É—auki sabbin ma'aikata na cike gurbi

Gwamnatin Neja dake da ma'aikata kusan 24,000 ta bayyana cewa ta É—auki sabbin ma'aikata 1,133 kuma matasa domin su cike guraben da take da su.

Galadima yace: "Mun ɗauki matasa 1,133 aiki domin su cike mana gurabe a ma'aikatu, da ɓangarori daban-daban masu matuƙar muhimmanci kamar ɓangaren lafiya, ilimi da kuma hukumar kashe gobara ta jihar."

Tsohon kwamishina a jihar Ondo, Joseph Ikpea, ya sha da ƙyar a hannun masu garkuwa da mutane, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa Ikpea yana cikin bacci wasu yan bindiga suka buÉ—e wa tawagar motocinsa wuta.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN