Soji a Sokoto sun sheke masu safarar makamai guda 3 zuwa Sabon Birni


Jami'an sojin Najeriya sun sheke masu safarar makamai guda uku a kauyen Naimaimai da ke kan iyakan Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Kakakin hukumar sojin Najeriya Janar Muhammed Yarima ya ce soji sun sheke masu safarar makaman ne ranar Talata daya ga watan Yuni. Ya ce mutanen suna gudanar da kasuwancin makaman ne a yankin Sabon Birni.

Ya ce soji sun kama makamai a lokacin kwanton bauna da suka yi a cikin daji tsakanin dajin Najeriya da jamhuriyar Nijar sakamakon samun ingantaccen bayanan sirri.

Daga cikin makamai da aka kama sun hada da bama baman RPG da chajar su, bindigogi kirar AK47 da wasu na'ukan makamai da albarussai.

Reported by ISYAKU.COM


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN