Rikici Ya Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamnan Anambra


Rikici ya ɓarke a jam'iyyar APC biyo bayan bayyana, Sanata Andy Uba, a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan Anambradake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani kuma gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shine ya bayyana sakamakom zaɓen a Otal ɗin Tuli, Awka d safiyar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan Abiodun yace Uba shine ya lashe zaɓen fidda gwani da ƙuri'u 230,201 yayin da ya lallas na kusa da shi, Johnbosco Onunkwo, wanda ya samu ƙuri'u 28,746.

Ngige yace Ba'a gudanar da zaɓen fidda ɗan takara ba

Ministan ƙwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa sama ba'a gudanar dazaɓen fitar da ɗan takara ba.

Ministan ba baiwa jam'iyyar APC shawar ta shirya zaɓen fitar da ɗan takara a ranar 29 ga watan Yuni.

Hakazalika, 11 daga cikin mutum 14 dake neman jam'iyyar APC ta tsayar da su takara sun bayyana cewa ba'a gudanar da zaɓen ba.

APC a Anambra ta yi watsi da sakamakon zaɓen da ake yaɗawa

A wani jawabi da kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Anambra, Okelo Madukaife, ya nesanta jam'iyyarsu da rahoton zaɓen da ake yaɗawa.

Yace: "An jawo hankalin mu kan wani rahoto dake yawo a kafafen watsa labarai ba tare da sanya hannun kowa ba, kuma ana danganta shi da sakamakom zaɓen fidda ɗan takara na jam'iyyar APC a Anambra."

"Sakamakon ba shi da alaƙa da zaɓen fidda ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Anambra, wanda kwata-kwata ba'a gudanar da shi ba."

"Muna jiran kwamitin riƙo na APC ta ƙasa ya saka ranar zaɓen cikin jadawalin da hukumar zaɓe ta fitar."

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN