Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC


Tsohon sakataren jam'iyyar APGA, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya sauya sheka daga jam'iyyar ya koma tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Mattawalle zuwa jam'iyyar APC mai mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Shinkafi tsohon dan takarar Gwamna na APGA kuma sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar a cikin wata wasika zuwa ga Sakataren Jam’iyyar na kasa ya sanar da murabus dinsa a matsayin memba na jam’iyyar kuma Sakataren kwamitin amintattu.

A cewar wasikar ta Shinkafi:

“Wannan shi ne a hukumance na mika takardar murabus a matsayin memba na jam'iyyar APGA kuma Sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar wanda zai fara daga ranar da wasikar ta kasance.
"Na yanke shawarar yin murabus ne bayan tuntuba da nayi da magoya baya na, da dangi na, da abokaina na siyasa a jihar ta Zamfara da sauran 'yan Najeriya wadanda suka samar da wani bangare na goyon baya na."
Ya nuna godiya ga Gwamnan Jihar Anambra wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APGA na kasa da kuma Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, Cif Willie Obiano da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Ya kara da cewa:

"Ina yi wa jam'iyyar fatan alheri da kuma Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyarmu a zaben gwamnan Anambra mai zuwa ranar 6 ga Nuwamba 2021, ina yi masa fatan samun nasara a zaben."#
Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC
Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyya mai mulki ta APC.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa:

"Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle."
Siyasar Kano: Jerin Wadanda Ake Kyautata Zaton Za Su Gaji Kujerar Ganduje a 2023
A wani labarin, Gabanin zaben gwamna a 2023 a jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce wakila da jam'iyya ne za su tsayar da wanda zai fito a matsayin wanda zai gaje shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Ganduje ya yi wannan bayanin ne bayan tsoffin ‘yan takarar gwamna uku a zabukan da suka gabata a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN