Ministan shari'a kuma babban Atoni janar na Najeriya Abubakar Malami SAN, ya ci gaba da taba rayuwar talakawan jihar Kebbi da alheri ta kungiyoyinsa na jinkai ga al'umma.
Malami, ta kungiyoyinsa na jinkai da taimakon al'umma ya bayar da kyautar takardar neman rubuta jarabawar JAMB kyauta ga yan asalin jihar Kebbi mutum 1000.
Kazalika kungiyar uwargidansa ta jinkai ta yi alkawarin yin koyarwar bita na JAMB kyauta ga wadanda suka amfana da kyautar Form na JAMB da aka bayar a fadin jihar.
Ministan shari:a ya umarci Malam Isiyaka Easy ya samar da cibiyoyi tare da tafiyar da tsarin koyarwar bita ga wadanda suka amfana da kyautar Form na JAMB a yankunan da aka ware domin tafiyar da shirin.
Kazalika, Malami ya samar wa jama'a rijiyoyin ruwa na borehole guda 236 a kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar Kebbi. Ministan ya tabbatar da haka ranar Asabar lokacin kaddamar da borehole da ya samar a sansanin wadanda rikici ya rabasu da muhallinsu da ke garin Ambursa.
Shirin taimakon al'umma na Malami, yana gudana ne da taimakon kungiyoyinsa na taimakon al'umma da na uwargidarsa wanda suka hada da Kadi Malami Foundation, Khadimiiya Initiative for Justice and Development, Aisha Abubakar Malami Centre for Women Development da Al-Iman Charity Foundation.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari