Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin Zungeru a jihar Neja tare da matansa biyu ranar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
An ɗauke Musatapha Madaki (Madakin Zungeru) tare da matan sa biyu da yammacin ranar Lahadi bayan wasu yan bindiga aƙalla 20 sun kutsa gidansa dake tsakiyar garin Zungeru.
Yan bindigan sun aje abun hawan su tsawon mita 500 da gidan hakimin, suka ƙarisa da kafafuwansu.
Maharan sun tafi kai tsaye zuwa gidan madakin, suka kutsa kai ɗakinsa suka fito dashi tare da matarsa ɗaya mai suna, Habiba.
Sun kuma yi awon gaba da matarsa ta biyu duk a wannan harin wanda maƙwabtan hakimin suka ce ya ɗauki kusan rabin sa'a ba tare da an kawo ɗauki ba.
Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan wasu yan bindiga sun kutsa cikin Islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, inda suka sace ɗalibai 156.
Legit.ng hausa ta gano cewa tsakanin Zungeru da garin Tegina bai wuce tafiyar kilomita 30 ba kacal.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari