Wata kotun Magistrate dake Ilorin ta bada izinin a cigaba da tsare wani Manomi mai suna Segun Adebayo Wanda ya harbe wani Makiyayi har lahira a gidan kaso da ke Oke-Kura.
Hukumar yan sandan tana tuhuman Adebayo da laifin kisa.
Mai Sharia Ibrahim Dasuki wanda ya bada izinin haka, Ya dage Zaman sauraro har zuwa June 22 inda zaa cigaba da sauraron karan.
Tun da fari ne, Lauya mai suna Inspekta Zachaues Folorusho lauya Mai kare wanda aka kashe, Ya bayyana ma Kotu cewa Dan uwan Mamacin mai suna Muhammad Adamu ya kawo ma 'yan Sanda rahoton Cewa dan uwansa fa bai dawo daga kiwo ba.
Dan Sanda ya bayyana Cewa wanda ake tuhuma wato Adebayo ya amsa laifin kisan da yayi, A dalilin ya kama Makiyayi yana kiwo a gonar sa.
Folorunsho ya kara bayyana cewa, Wanda ake tuhuma ya amsa laifin shi ya kashe wannan matashi mai Shekara Sha takwas, A inda yayi kokarin boye gawan.
Ya roki Alfarmar kotu data cigaba da tsare Mai laifin domin laifinsa ya fi karfin beli.
Haka zalika Jaridar pulse.ng, ta bayyana cewa wanda ake tuhuma bai yi musu ba ya amsa laifin sa.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari