Da dumi-dumi: APC ta dakatar da Sharada, dan majalisar mai adawa da Ganduje


Jam’iyyar All Progressives Congress jihar Kano ta dakatar da Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, dan majalisar wakilai da ke wakiltan yankin karamar hukumar birni da kewaye na Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An dakatar da Sharada wanda ke sukar Gwamna Abdullahi Ganduje na tsawon shekara daya.

Jaridar Daily Nigerian ta kuma ruwaito cewa an dakatar da Sharada ne bisa zarginsa da ayyukan da suka saba jam’iyya.

An tattaro cewa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai da aka kafa domin binciken zarge-zargen da ake yi masa sun same shi da laifi.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa an haramtawa Sharada shiga dukka harkokin jam’iyyar a dukkan matakai.

An samu Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da aikata laifin da ake tuhumarsa da shi na kisan halayyar mai girma Gwamnan Kano da kuma shugabannin jam’iyya daban-daban daga shiyya, Karamar Hukuma da Matakin Jiha.

 "Cewa ba zai tsoma baki a dukkan harkokin jam'iyyar da ayyukanta ba a dukkan matakai," kamar yadda wasikar da kwamitin ya karanta.

A wani labarin, tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya caccaki gwamnoni a Najeriya yana mai cewa sun lalata dimokiradiyyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Na’Abba, yayin da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Talata, ya ce gwamnonin jihohi sun lalata dimokiradiyya, suna yin magudi a zabukan fidda gwani na jam’iyyunsu na siyasa don wanda suke so ya fito.Y

Yakara da cewa gwamnonin sun kuma toshe damar da matasa za su iya shiga siyasa "wanda hakan babbar barazana ce ga makomar kasar."

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN