Yan bindiga sun farmaki Gundumar Kambuwa a karamar hukumar Ngaski da wasu kauyuka a karamar hukumar Shanga suka kora shanayen bayin Allah da ba a tantance yawansu ba kawo yanzu.
Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa da tsakiyar ranar Talata 1 ga watan Yuni yan bindigan suka farmaki garuruwan Maburo, Shagiya, Arabu lafiya, Daban kurege, da Tungan hantsi.
Rahotanni sun ce jama'a sun kaurace wa gidajensu a Kambuwa da Bunu kuma suka sami mafaka a kauyen Kimo. Kawo yanzu dai babu cikakken kididdigan irin ta'asar da Yan bindigan dajin suka aikata a kauyukan da suka kai farmaki.
Sai dai wata majiya ta tsaro mai tushe a jihar Kebbi, ta tabbatar da cewa Yan bindigan daji sun farmaki Kambuwa a karamar hukumar Ngaski da wasu kauyuka a karamar hukumar Shanga ranar Talata 1 ga watan Yuni, suka kora shanayen jama'a daga bisani suka tafi.
Rahotun Abdullahi Musa, Isyaku Garba Zuru.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI