Yansanda jihar Kebbi sun gano gawar Dan jihar Katsina a dakinsa a Gwadangaji

Illustrative

Yansandan jihar Kebbi sun sami gawar wani matashi a cikin gidansa da ke rukunin gidajen Aliero a garin Gwadangaji da ke makwabta da garin Birnin kebbi ranar Litinin.


An sami gawar Kamal Muhammad a cikin dakinsa bayan makwabta sun jiyo wari yana bugawa daga gidansa da yake zaune shi kadai.

Lamari da ya haifar da zargin cewa wata kilan Kamal ya rasu ne yan kwanaki kafin ranar Litinin 31 ga watan Mayu.

Marigayin dan shekara 38 a Duniya Dan asalin garin Funtua ne da ke jihar Katsina, kuma ma'aikacin hukumar Federal Inland Revenue Service FIRS a jihar Kebbi.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya tabbatar da faruwàr lamarin. Nafi'u ya ce " Hukumar yansandan jihar Kebbi na sane da aukuwan lamarin kuma yanzu haka Kwamishinan yansandan jihar Kebbi ya bayar da umarnin gudanar da bincike a sashen CIID".

" Muna jiran rahotun sakamakon binciken Likita kan musabbabin mutuwarsa" Inji DSP Nafi'u Abubakar.

Sai dai shafin ISYAKU.COM ya samo cewa babu jini a jikin gawar Kamal ko a cikin dakinsa akasin yadda ake jita jita a shafukan sada zumunta, da kuma Labarin haka da ke yawatawa a garin Birnin kebbi.

Rahotun Maryam Muhammad, Isyaku Garba Zuru.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN