Kungiyoyi masu fafutikan kare hakkin arewa karkashin Hadakar Kungiyoyin Arewa, Coalition of Northern Groups, CNG, a ranar Talata sun gargadi basarake Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Otunba Gani Adams, kan kashe yan arewa a Kudu maso Yamma, The Punch ta ruwaito.
Tribune ta ruwaito cewa kungiyar ta ce gargadin ya zama dole biyo bayan kalaman da aka danganta da Adams na cewa kashe mutane a Igangan, Ibarapa a Oke-Ogun a jihar Oyo, tamkar yaki ne Arewa ke son yi da Kudu maso Yamma.
CNG ta yi wannan gargadin ne ta bakin kakinta, Abdul- Azeez Suleiman.
Ya ce, "Ba za mu amince da duk wani hari da za a kaiwa yan arewa a kudu ba saboda kasancewarsu kawai yan arewa."
Suleiman ya ce CNG ta yi mamakin yadda Gani Adams duk da matsayin da ya ke rike da shi a kasar Yarbawa, "ya gaza yin watsi da halinsa na baya na dan daba ya rungumi dattaku irin na sarauta."
"Munyi mamakin ganin yadda Adams ya danganta harin da yan arewa duk da cewa hukumomi ba su gano ainihin wadanda suka kai harin ba.
"Gagawar da Adams ya yi na danganta cewa yan arewa ne suka kai harin har ma da neman ambaton yaki ya nuna yadda zuciyan 'yan kudu' ta ke na kin yankin arewa," in ji CNG.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari