Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya ce zai shiga daji domin ceto ɗaliban makarantar garin Yauri da ƴan bindiga suka sace.
Gwamnan ya yi wannan alwashin ne gaban mafarautan jihar Kebbi inda ya ce“Na kira gayya kuma za mu shiga daji.”
Ya kuma faɗa wa mafarautan cewa su tafi su shirya kafin ya yi magana da shugabannin jami’an tsaro. Ya ce an zaɓe su ne ba don su yi zauna a ofis ba,
“Dama Kur’ani aka ba mu mun ka yi rantsuwa kuma ba mu yi rantsuwa ba don mu zauna a ofis ba,” in ji shi.
A ranar Alhamis ne ƴan bindigar suka kutsa Kwalejin Yawuri suka sace ɗalibai da dama.
Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto wasu daga cikin ɗaliban, tare da kashe ƴan bindiga da dama.
Rahotanni sun ce an yi gumurzu sosai tsakanin jami’an tsaro da ɓarayin dajin a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi.
Rahotun BBC
Hotuna: KBGH
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari