Shugaba Buhari ya buƙaci kamfanin MTN ya rage rarashin 'Data' ga yan Najeriya


Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga kamfanin sadarwa na MTN da su rage farashin sayen 'Data' ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Buhari yayi wannan kira ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin kamfanin, ƙarkashin jagorancin shugaban MTN, Ralph Mupita, a fadar sa dake Abuja.

Buhari ya tabbatar wa kamfanin MTN cewa gwamnatinsa zata yi duk me yuwu wa domin samar da kyakkyawan wuri na yin kasuwanci a Najeriya.

Buhari yace: "Najeriya ce ƙasar da kuka fi samun garabasar kasuwanci a Africa, Asia da sauran su, kuma ita ce ƙasa ta uku da kamfanin MTN yafi samun kuɗin shiga. Sabida haka, muna roƙon ku, ku sauƙaƙa wa yan Najeriya masu amfani da MTN."

MTN yace za'a samu ƙasarancin sabis sabida matsalar tsaro

A ranar laraba, shugaban MTN Nigeria, Karl Toriola, ya bayyana cewa kwastomomi ka iya fuskantar karancin sabis a Najeriya saboda ƙaruwar matsalar tsaro.

Kamfanin sadarwar na MTN ya kara da cewa zai yi iyakacin ƙoƙarinsa ya tabbatar da an samu ingantaccen sabis da zai wa yan Najeriya aiki yadda suke buƙata.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC a Kebbi Sama da 80

Sojoji sun kashe yan bindiga sama da 80, waɗanda suka sace ɗaliban makarantar FGC Birnin Yauri, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Shaidu sun bayyana cewa jami'an sojin sun yi amfani da dabarar yaƙi, inda suka yi wa ɓarayin kofar rago.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN