Duba matsayar da aka cimma tsakanin ƙabilar Igbo da ƴan kasuwar arewa


Wasu shugabannin al'ummar Igbo ƙarƙashin jagorancin fitaccen attajirin nan, Cif Emmanuel Iwuanyanwu sun buƙaci 'yan arewacin ƙasar da ke kasuwanci a Kudu masu Gabas, su yi musu cikakken bayani na ƙiyasin asarar da aka yi musu a hare-haren masu rajin kafa ƙasar Biafra.

Matakin wani ɓangare ne na wani taro da shugabannin suka yi da 'yan kasuwar arewa da ke harkoki a kudu maso gabas.

Ana zargin 'ya'yan ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya da kai hare-hare kan harkoki da cibiyoyin gwamnati da jami'an tsaro da kuma ɗaiɗaikun mutane ciki har da mutanen arewa.

A ranar Litinin 21 ga watan Yuni ne aka gudanar da taron a birnin Owerri na jihar Imo, kuma ya samu halartar ɗumbin masu faɗa a ji daga ƴan kasauwa ƴn kabilar Igbo.

Alhaji Ya'u Ali shugaban masu sayar da dabbobi na arewa ya ce babban abin da ya sa suka halarci taron shi ne don a ɗauki mataki kan kisan ƴan arewa da ake yi a kudu maso gabas ɗin.

Ga dai jerin abubuwan da aka cimma a taron:

1. Mahalartar taron ƴan ƙabilar Igbo sun yi na'am da ganawar tare da shan alwashin yin duk abin da ya dace don tabbatar da cewa sun kare lafiya da dukiyoyin ƴan arewa mazauna yankinsu.

2. Cif Emmanuel Nwuanyanwu ya yi alkawarin cewa manyan ƙabilar za su tabbatar da komawar al'amura daidai kamar yadda aka saba.

"Idan akwai ƴan Najeriya masu gaskiya ya kamata mu agaza musu, da zarar muna da mutane irin kuna yi musu magana, ya kamata mu taimaka musu.

3. Ƴan arewan na so a biya diyyar waɗanda aka kashe a rikicin kwanan nan.

4. Manyan ƙabilar Igbon sun ce za su sake kiran wani babban taron a arewa, kuma nan da wata guda komai zai daidaita.

5. An buƙaci ƴan arewan su kai rahoto kan dukkan asarar da aka yi musu ta kashe-kashe da ɓarnata dukiya.

A kwanakin baya wasu masu faɗa a ji daga cikin ƙabilar Igbo sun bayyana fargaba kan yanayin da ake ciki, ganin irin yadda dukiyoyin ƴan ƙabilar Igbon ke warwatse a yankuna daban-daban na arewacin Najeriya.

Sun nuna a ƙalla akwai mutum miliyan 11 ƴan ƙabilar Igbo da ke zaune a arewacin Najeriya.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN