Kotu ta tura masoya gidan gyara hali sakamakon hulda da ya kai ga daukan ciki a Birnin kebbi


Wata Kotun Majistare a garin Birnin kebbi ranar Talata, ta tasa keyar wani masoyi mai suna Onyebuchi Okafor da masoyiyarsa Mansura Shehu zuwa gidan gyara hali sakamakon tuhumar aikata lalata da yavkai ga daukan ciki.


Alkalin Kotun Samaila Kakale Mungadi ya ki amincewa da neman belin da Lauyan wanda ake tuhuma Onyebuci mai suna Magnus Ihejirika ya gabatar da baki. Ya umarci Lauyan ya gabatar da bukatar neman belin a rubuce. NAN ta ruwaito.

Mai gabatar da Kara na yansanda ya shaida wa Kotu cewa ana tuhumar masoyan biyu ne bayan Mansura ta dau cikin na gaba da fatiha, sakamakon huldar soyayya da Onyebuchi. Wanda haka ya saba wa sashe na 369 na dokar Penal Code.

Kotu ta dage shari'ar har ranar 5 ga watan Juli domin ci gaba da sauraron shari'ar.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN