Wani gagarumin gwanin nutso a kasar Amurka ya sha da kyar bayan da kifi ya hadiye shi kuma cike da sa'a ya amayo shi.
Mutumin mai suna Michael Packard mai shekaru 56 yace yana da tsananin sa'a tunda ya rayu bayan farmakin da kifin ya kai masa yayin da yake aikinsa na kullum a Massachusetts.
Daily Mail ta ruwaito cewa mutumin ya bada labarin yadda komai ya koma masa bakikkirin yayin da yake cikin kifin.
Da farko yace zatonsa shark ne ya kai masa farmaki amma a lokacin da bai ji hakoransa ba, sai ya gane cewa ba shark bane.
"Na gano cewa bakin kifi Whale nake ciki kuma yana kokarin hadiye ni. Daga nan na fara tunani, shikenan na mutu," ya bada labari.
The Insider ta ruwaito cewa mutumin ya tabbatar da cewa ya kwashe dakika 30 zuwa 40 a cikin kifin amma cike da sa'a aka samu ya amayo shi.
"Kawai na ji an watso ni a iska kuma na fada ruwa. Dagan nan na gane na fito. Ga ni nan ina bada labarai," Packard yace.
Wani mutum dake tare da mutumin mai shekaru 56 shi ya taimaka masa wurin fitar dashi daga ruwan. Duk da bai ji ciwo ba, ya dai samu guggurjewa a jikinsa.
A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya, ta yi amfani da jirginta na Alpha inda ta ragargaji wuraren garin Genu dake jihar Neja, lamarin da ya kawo mutuwar wasu 'yan bindiga tare da tserewar wasu.
PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin shanun satan da 'yan bindigan suka sato daga sansanin sojoji a jihar Katsina duk sun mutu.
Daya daga cikin bama-baman ya fada wurin liyafar biki a wani kauye dake da kusanci da garin, kamar yadda ganau suka tabbatar.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari