Wani dalibin Najeriya mai suna Iniobong Ekpo, ya shigar da jami'ar jihar Akwa Ibom kotu kan korarsa da tayi kan abin da ya daura a kafar ra'ayi da sada zumunta na suka gwamnan jihar, Udom Emmanuel.
A cewar Soaznews Etv, jami'ar ta bayyana korar dalibin a wasikar da ta aike ranar 9 ga Afrilu, 2021 saboda rashin da'ar da ya yi. Hakazalika tace wannan ya sabawa dokar jami'ar.
Rijistarn jami'ar Joh E Udo, wanda ya rattafa hannu kan wasikar ya kara da cewa an haramtawa dalibin shiga jami'ar.
Yanzu haka ya shigar da jami'ar kotu kuma ya bukaci a biyashi kudi N20m, kuma a rabu da shi ya cigaba da karatunsa.
Abinda dalibin da daura a Facebook
Premium Times ta ruwaito cewa dalibin wanda ke karatu a tsangayar injiniyancin aikin noma ya tuhumci gwamnan da laifin rashin cika alkawarin da yayi daliban da aka yaye a 2017.
Yace:"
Shekaru biyu da kwanaki 166 bayan alkawarin da yayi, har yanzu babu ko mutum guda cikin daliban da aka yaye da ya samu ko Naira guda duk da cewa wadanda suka fita da 1st Class sun je ofishinsa amma basu gansa ba."
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari