Ta faru ta kare: Wata amarya ta kashe ango bayan cacan baki, duba yadda ta faru


Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke wata mata mai shekara 25, Hadiza Musa kan zargin aikawa da mijinta barzahu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamun kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Ya ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata a kauyen Maradawa da ke karamar hukumar Kazaure.

Sashin Hausa na BBC ma ta ruwaito cewa rundunar yan sandan ta ce ta fara gudanar da bincike kan matar da ake zargin ta aikata wannan laifin bayan wata hatsaniya ta barke a tsakaninsu.

Adam ya ce wanda abun ya cika da shi ya samu rauni a kansa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Ya ce an kai mamacin babban asibitin Kazaure inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Source: Legit

https://youtu.be/xRYphqBjqwc

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN