Kamfanonin sadarwa a Najeriya kamar MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara rufe amfani da damar shiga dandalin sada zumunta twitter, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kamfanonin sun ce sun samu saƙon umarni daga hukumar sadarwa ta ƙasa NCC cewa su tsayar da damar shiga twitter a ƙasa biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da shafin.
Yan Najeriya masu amfani da twitter sun wayi garin ranar Asabar ba tare da samun damar amfani da shafinsu na twitter ba, yayin da wasu ke amfani da wata manhajar sadarwa domin shiga shafin su.
Kamfanonin sadarwar Najeriya baki ɗaya sun bayyana ƙarƙashin ƙungiyar su cewa sun fara dakatar da damar amfani da twitter a wani jawabi da suka fitar ranar Asabar.
Jawabin wanda a ka yiwa take da "Umarnin dakatar da mafani da twitter a Najeriya" wanda shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, da sakatarensa, Gbolahan Awonuga, suka sanya wa hannu.
Wani sashin jawabin yace: "Mu, Ƙungiyar kamfanonin sadarwa ALTON, mun tabbatar da mambobin mu sun samu umarni daga NCC cewa su dakatar da bayar da damar amfani da twitter."
"Mambobin mu sun yi biyayya ga umarnin da hukumar sadarwa NCC ta basu, kuma zasu cigaba da biyayya ga dukkan umarnin da hukumomi da masu faɗa aji suka basu a Najeriya."
A wani labarin kuma
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari