Da duminsa: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ayyukanta a Najeriya, ta sanar da matakin dauka


Twitter ta bayyana tsananin damuwarta bayan hukuncin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukanta a Najeriya.

Sarah Hart, babbar manajan yada labarai ta Twitter na Turai, gabas ta tsakiya da Afrika ta sanar da TheCable cewa kamfanin na duba wannan cigaban.

TheCable ta ruwaito yadda gwamnati ta dakatar da ayyukanta bayan zargin kafar sada zumuntar da goge wani tsokacin shugaban kasa.

A wata takarda da Lai Mohammed, ministan yada labarai ya fitar a ranar Juma'a, yace dole ce ta sa gwamnati ta yi abinda tayi saboda ana amfani da kafar wurin kaskanci ga Najeriya.

Amma kuma har a lokacin rubuta wannan rahoton, kafar na nan tana aiki a Najeriya.

A wani sakon yanar gizo, Hart ta ce: "Sanarwan da Najeriya tayi na dakatar da ayyukanta a Najeriya abun damuwa ne.

"Muna bincike kuma zamu sanar da halin da ake ciki idan muka kammala."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kushe yadda wasu bata-gari ke kaiwa kadarorin gwamnati hari a yankunan kasar nan. Ya yi barazanar yi musu amfani da abinda suka fi ganewa inda ya alakanta hakan da yakin basasa.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN