Mahukunta sun kama wata mata bisa zargin kashe mijinta tare da yanke mazakutarsa kuma ta soya a kasar Brazil.
Yansanda sun kama Uwargida mai suna
Dayane Cristina Rodrigues Machado, yar shekara 33, a birnin Sao Goncalo ranar 7 ga watan Yuni.
Rahotanni sun ce matar ta kashe mijinta ne da karfe 4 na safe bayan zafafar muhawwara da suka yi domin kawo karshen aurensu na shekara 10.
Yansanda sun sami wuka a gefen gawar mijinta mai suna Andre kwance tsirara a tsakiyar daki. Ana kyautata zaton cewa ta yi amfani da wukar ne ta kashe Andre.
Wani abin mamaki shi ne yadda wannan mata ta yanke al'aurar Andre kuma har ta soya da man wake soya bisa dalili da ita kadai ta san manufar yin haka.
Ma'auratan suna da yara biyu kafin mutuwar mahaifin su Andre a hannun mahaifiyarsu.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari