Da Dumi-Dumi: Rikici Ya Barke a Wurin Taron Jam'iyyar APC a Kano


An samu barƙewar rikici a wurin taron gangami na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Taron da ake yi a yankin Sabon Gari na jihar Kano, an shirya shi ne domin tarbar tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar Green Party of Nigeria, GPN, A.A. Zaura da wasu mutane da suka sauya sheka zuwa APC.

A yayin da kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt Hon Hamisu Chidari ke yin jawabinsa, wasu mambobin jam'iyyar suka fara bawa hammata iska.

Daily Trust ta ruwaito cewa fadar da ta kaure tsakanin su ta kusa tarwatsa taron a yayin da mutane suka fara dare wa don gudun kada a raunata su.

Sai dai bayan ɗan wani lokaci an dakatar da faɗan kuma abubuwa sun koma yadda suke.

A halin yanzu ana cigaba da taron.

Ku saurari karin bayani ...

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN