Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah


Hukumomin kasar Saudiyya sun ce mazauna cikin kasar ne kadai za a bari su gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar.

A cewar wata sanarwa da mahukuntan Masallacin Harami suka wallafa a shafin Facebook na masallacin, ta ce mutum dubu 60 ne kadai za a bari su gudanar ibadar Hajjin sakamakon annobar COVID-19 da duniya ke fuskanta a halin yanzu.

“Bisa la’akari da annobar Covid-19 da ke ci gaba da addabar kasashen duniya da kuma bayyanar sabuwar cutar, Hajjin shekarar Musulunci ta 1442 zai takaita ne ga ‘yan kasar Saudiyya da mazauna cikin kasar kadai. Mutum dubu 60 ne kadai za su gudanar da ibadar,” kamar yadda sanarwar ta nunar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mahajjatan da za a bari su gudanar ibadar dole ne mutum ya zama wanda ya yi rigakafin cutar Covid-19 akalla sau daya sannan ya yi kwana 14 da karbar allurar ko kuma mutumin da ya murmure daga jinyar kuma aka masa rigakafin cutar.

Idan za a iya tunawa ko a bara mahukuntan Saudiyyar sun hana mahajjata daga kasashen wajen shiga kasar domin gudanar da aikin Hajjin sakamakon annobar ta Covid-19, inda aka zabo wadansu mutum kasa da dubu 10 suka gabatar da Hajjin.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN