An yi ma wasu tsofaffin mata masu shekara 75 da mai shekara 91 fyade a gidansu da ke igubudwini Administrative Area a Tsomo, wanda ke gabacin Cape, a kasar Afrika ta kudu a cikin daren Asabar 6 ga watan Yuni.
Wasu mutane sun shiga gidan tsofaffin cikin dare yayin da suke barci. Sun tsallako ta tagar dakin da suke kwance suka karbe kudadensu daga bisani suka yi masu fyaden fitan albarka.
Wannan lamari ya yi sanadin mutuwar tsohuwa mai shekara 91. Yayin da mai shekara 71 ta samu ta tsere zuwa gidan makwabta ta nemi taimako.
Yansanda sun tarar da gawar tsohuwa yar shekara 91 a weje. Kuma yan fashin sun tsere.
Brigadier Tembinkosi Kinana, jami'in hulda da jama'a na SAPS, ya ce ko da suka zo sun tarar tsohuwar mai shekara 91 ta riga ta mutu.
Ya ce sun dukufa wajen neman wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin kama su a hukunta su.
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari