Abin da ya kamata ku sani yayin da Tashar Arewa 24 ke bikin cika shekara 7 da kafuwa


Tashar talabijin ta Arewa 24 ta bayyana cewa tana yaÉ—a shirye-shiryenta ga masu kallo miliyan 40 a Najeriya da Yammacin Afirka, a cewar tashar wadda ke bikin shekara bakwai da kafuwa.

Tashar wadda ke da babban ofishi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a yau Litinin 28 ga watan Yunin 2021, ta cika shekara bakwai cur da kafuwa.

Arewa 24 tasha ce da ke yaɗa shirye-shiryen da suka shafi rayuwar Hausawa ta yau da kullum cikin harshen Hausa - saɓanin kafofi irinsu BBC Hausa da ke yaɗa labarai kawai.

Wata sanarwa daga tashar ta ce an kafa ta ne "domin cike wagegen giɓi" a arewacin Najeriya.

Labarina Series: Yadda mai hakuri ta dafa dutse ta sha romonsa
Fina-finai masu dogon zango da sauyin da suka kawo a Kannywood
Gidan Badamasi a mahangar nazari

"An kafa tashar Arewa 24 a shekarar 2014 domin cike wawakeken giɓin da ake da shi a fagen shirye-shiryen nishaɗi da tsarin rayuwa da ake shiryawa da harshen Hausa, waɗanda ke nuni da abubuwan da ake alfahari da su a rayuwar Arewacin Najeriya da al'adu da kaɗe-kaɗe da fina-finai da fasaha da girke-girke da kuma wasanni."

Shugaban Arewa 24, Jacob Arback ya ce: "Mutane da dama ba su fahimci cewa akwai mutane masu magana da harshen Hausa sama da milyan 80 a Arewacin Najeriya da kuma yankin Sahel ba, kuma yankin na cike da matasa masu basira a ko'ina.

"Sai dai abin da na fi alfahari da shi, shi ne yadda hukumar gudanarwa da ma'aikatanmu suka tattaru daga bangarori na rayuwa daban-daban da addinai da ƙabilu da kuma yankunan Najeriya daban-daban."


Tashar na da É—umbin mabiya a shafukan sada zumunta da suka haÉ—a da Facebook (1,397,067) da Twitter (124.5K) da Instagram (1.7k).

Baya ga shirye-shirye na yau da kullum, tashar Arewa 24 na nuna fina-finai na Kannywood ko kuma na ƙasashen waje waɗanda aka fassara da Hausa.

Fina-finai masu dogon zango irin su Dadin Kowa da Labarina da Gidan Badamasi, su ne suka ƙara wa tauraruwar Arewa 24 haske.

Miliyoyin masu kallo, maza da mata da matasa da tsofaffi, na bin irin waÉ—annan fina-finai da ake nunawa mako-mako.

Kazalika, akwai fim É—in Kyautata Rayuwa - fim É—in Turkiyya wanda aka fassara da Hausa - da kuma wasu na Indiya.

Shirin nishaɗsntarwa mai suna Zafafa 10 da Aminu Abba Umar - wanda aka fi sani da Nomiss G - ke gabatarwa yana jan hankalin matasa matuƙa. Shirin yana duba fitattun waƙoƙin Hausa Hip-Hop tare da hira da masu buga su.

Presentational grey line
Daga cikin sabbin shirye-shiryen da tashar ta yi wa masu kallo alƙawari da za ta fara gudanarwa a watan Yuli mai kamawa akwai:

Buka Africana - fim mai dogon zango
Labarina zango na 3 - fim mai dogon zango
Mata a Yau - shiri kan harkokin mata
Ana kama tashar Arewa 24 a kan tauraron É—an Adam a layukan StarTimes da DSTV da TSTV da Canal+ da Gotv a kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Chadi da kuma Kamaru. Haka nan, ana kama su ta intanet a kan manhajar Arewa 24 On Demand.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN