Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC


Rahotanni sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Zamfara Matawalle zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC gobe.

A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar The Nation ya ce, mai magana da yawun gwamnan, Mista Yusuf Idris, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa gwamnonin APC 18 za su yi maraba da shi.

Ya bayyana cewa:

"Yanzu an gama komai domin gwamnanmu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC."

A cewarsa, gobe za a yi kasaitaccen liyafa a Gusau, babban birnin jihar.

Idris ya ce

"Gwamnan zai zo tare da dukkan mambobin majalisar kasa da na jihar gami da shugabannin jam'iyyar PDP daga dukkan matakan jihar."

Yayi imanin ficewar gwamnan zai karfafa jam'iyyar APC a jihar.

“‘Yan siyasar Zamfara sun kasance 'yan gida daya kuma a matsayinsa na gwamnan PDP, yana da kyakkyawar alaka da wadanda ke cikin jam’iyyun adawa.
“Mutane da yawa daga manya har kanana sun bi gwamnan zuwa PDP domin bayar da shawarwarinsu na kwarai don ci gaban jihar.
"Wasu daga cikin irin wadannan an ba su manyan mukamai da matsayi na gwamnati wadanda suka rike su da kyau."

Sauran wadanda suka sauya shekar sun hada da Gwamna Dave Umahi na Ebonyi da Ben Ayade na Kuros Riba.

Tare da ficewar Matawalle, adadin gwamnonin PDP ya ragu daga 16 zuwa 13. APC yanzu tana da jihohi 23 a karkashin ikonta.

PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

A wani labarin, Majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a gobe zai koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan yasa PDP ta ce za ta dauki matakin doka domin dakatar da gwamnan na Zamfara daga barin jam'iyyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba, an tattaro cewa za a ambaci karar da wasu jiga-jigan PDP suka shigar kan sauya shekar Matawalle a yau a kotu.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN