Yansanda sun kama wadanda suka sace yaro suka karbi N1m suka kashe shi a KadunaRundunar yansandan jihar Kaduna ta kama mutum 3 da ake zargi da sace yaro mai shekara 6 suka karbi kudin fansa Naira miliyan daya daga bisani suka kashe shi a jihar Kaduna.

Binciken yansanda ya nuna cewa makwabcin mahaifin yaron mai suna Muhammadd Kabir ne ya kitsa sace yaron daga unguwarsu ta Badawa a Kaduna.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya ce bayan mutanen uku sun sace yaron, sun kai shi Kano kuma suka bukaci kudin fansa. Ya ce sun kashe yaron ne domin zai iya gane makwabcin nasu kuma zai iya fallasa shi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari