Yansanda sun kama soji da ya kashe mai mota da ya rage masa hanya, kuma ya tsere da motar

J

ami'an Rundunar yansandan jihar Akwa Ibom ta kama wani jami'in soji bisa zargin kashe wani dan kasuwa kuma ya tsere da motarsa.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi 23 ga watan Mayu a karamar hukumar Ikot Abasi bayan dan kasuwan ya tsaya ya taimaka wa sojin don ya rage masa hanya. Sai dai suna cikin tafiya sai sojjn ya bukaci mai motar ya tsayar da motar.

Rahotanni sun nuna cewa sojin ya kashe mai motar kuma ya shiga motar ya tsere da ita bayan ya jefar da gawar mai motar a gefen titi.

Iyalin mai motar sun kai kara wajen yansanda bayan an tsinci gawarsa, kuma suka gaya wa yansanda cewa motar tana da na'urar da za a gano wajen da motar take watau Tracking device.

Da trackin device da ke cikin motar yansanda sun gano wajen da motar take a karamar hukumar Ukanafun ranar 25 ga watan Mayu.

Kakakin hukumar yansandan jihar Akwa Ibom, Odiko Macdon, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda sun gano motar a hannun sojin da suka kama a karamar hukumar Ukanafun. Ya ce an sami bindiga kirar AK47 tare da sojjn lokacin da aka kama shi.
Ya Kara da cewa yansanda na ci gaba da gudanar da bincike bayan sun kai gawar mai motar dakin adana gawa a Asibiti.






Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN