'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan-Sakai 19 a Ƙauyen Jihar Sokoto


Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

"Sun zo ne da nufin kashe ɗaya daga cikin shugabannin ƴan sa-kan a yankin," in ji shi.

An ruwaito cewa ƴan bindigan sun halaka shugaban ƴan sa-kan (da aka ɓoye sunansa) a gonarsa.

Kansilar Ghandi A, Aminu Mua'azu Ghandi shima ya tabbatar da afkuwar lamarin lokacin yana mai cewa 14 cikin yan sa-kan ƴan Ghandi ne sauran biyar ɗin kuwa ƴan wasu garuruwa ne da ke karkashin Ghandi.

Ya ce wasu mutum 5 da aka yi wa munanan rauni a harin suna asibiti ana musu magani

Ya kara da cewa yan bindigan sun sace dabbobi da dama da yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar, yayin tabbatar da harin ya ce mutum 10 ne kawai suka mutu cikin ƴan sa-kan.

A cewarsa, yan bindigan sun so shiga ƙauyen Yartsakuwa amma aka dakile harin.

Ya ce bayan yan sa-kan, babu wani mahaluki da aka kashe a garin.

Ya shawarci ƴan sa-kan su rika jiran ƴan sanda kafin su tunkari ƴan bindigan.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN