Yansandan jihar Sokoto sun kubutar da wata yarinya mai suna Joy Emmanuel yar shekara 12 da aka daureta aka killace ta har tsawon wata 8 a gidansu da ke Unguwar Sokoto Cinema a karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Kakakin yansandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Rahotanni sun yi zargin cewa iyayen yarinyar Bassey da Esther Emmanuel sun daure yarinyar ne bisa dalilan tabin hankali.
Yansanda sun ceto yarinyar ranar Alhamis 13 ga watan Mayu kuma an kama iyayenta aka kulle su a ofishin yansanda na Dadin kowa da ke Sokoto yayin da ake ci gaba da binciken lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI