Janar Mahamat Idriss Deby: Abubuwan da Buhari shugaban Chadi suka tattauna


A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Chadi Laftanar Janar Mahamat Idriss Deby a Abuja, inda suka tattauna game da ci gaban ƙasashensu.

Wannan ne karon farko da Janar Mahamat mai shekara 37 ke ziyara a Najeriya tun bayan da ya gaji mahaifinsa Idris Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Chadi a watan Afrilu.

A farkon watan Mayu ne Janar Mahamat ya kai irin wannan ziyara Jamhuriyar Nijar. Muhimmancin ziyarar na da girman gaske ganin yadda ƙasashen uku ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi baya ga iyakoki da suka haɗa.

Dawo da dimokuraÉ—iyya a Chadi

Buhari da Mahamat Idris Deby

ASALIN HOTON,NIGERIA PREIDENCY

Shugaba Buhari ya faÉ—a wa Janar Mahamat cewa Najeriya za ta tallafa wajen daidaita Chadi da kuma tabbatar da komawarta kan tsarin mulkin dimokuraÉ—iyya.

"Najeriya ta san irin rawar da Chadi ta taka wajen taimaka mata a yaƙi da ta'addanci kuma muna godiya sannan za mu ci gaba da wannan alaƙar", in ji Buhari.

"Nahiya da al'adu sun haɗa ƙasashenmu waje guda, saboda haka za mu taimaka a cikin duk abin da za mu iya".

Buhari ya kuma bayyana mahaifin sabon shugaban Chadin wato Idris Deby Itno a matsayin abokinsa kuma abokin Najeriya.

Tsaurara tsaro a Tafkin Chadi

Buhari da Mahamat Idris Deby

ASALIN HOTON,NIGERIA PRESIDENCY

Ƙasashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru na cikin hukumar kula da Tafkin Chadi mai suna Lake Chad Basin Commission (LCBC), wadda aka kafa don kula da kuma haɓaka shi.

Buhari ya tabbatar wa da takwaran nasa cewa Najeriya za ta ci gaba da ayyukanta a ƙungiyar tsaron haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ta MNJTF.

Alaƙar Buhari da Idriss Deby

Buhari da Mahamat Idris Deby

ASALIN HOTON,NIGERIA PRESIDENCY

A jawabinsa, Janar Mahamat Idriss Deby ya gode wa Najeriya bisa irin goyon bayan da aka nuna musu bayan mutuwar mahaifinsa kuma tsohon shugaban Chadi.

"Kana cikin na kusa-kusa ga Marshal Itno. Na zo ne domin na ƙarfafa wannan alaƙar da kuma neman ka taimaka mana wajen shugabancinmu.

"Mun dogara a kan 'yar uwarmu Najeriya kamar yadda muka haÉ—a al'ada da nahiya. A shirye muke mu yi amfani da taimakonka don komawa kan tsarin dimokuraÉ—iyya."

Ya kuma sake nanata kudirinsa na ganin an gudanar da sahihin zaɓe nan da wata 18.

Rahotun BBC Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN