Yan sanda sun gargadi Bokaye kan ba ‘Yan ta’adda Layu


Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi ta gargadi bokaye kan taimaka wa ‘yan ta’adda ta hanyar basu layu domin aikata ayukkan ta’addanci.

DSP, Lobeth Odah, jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ya bayyana hakan a ya yin wata hira da kanfanin dillancin labarai na kasa wato NAN, ranar Juma’a a Abakaliki.

DSP, wanda ya bayyana yunkurin rundunar ‘yan sanda na kare dukiyoyi da rayuwar al’umma, ya ja hankalin bokayen da su guji haramtattun huldodi na bokancin taimakawa mabarnata.

A watan Aprilun baya dai, rundunar ‘yan sandan ta gano wasu kaburburan mutum biyu a wani dajin Agubia na karamar Hukumar Ikwo, wanda wasu bokaye su ka bizne bayan yin garkuwa da su.

Tuni dai ‘yan sandan sun cafke bokayen da ake zargi da aikata yin garkuwa da mutanen tare da kasha su, in ji DSP Odah a cikin hirar.

“Mun yi anfani da masana muka tafi dajin, kuma an yi nasarar ciro mutanen daga inda aka bizne su, mun mika su ga ‘yan uwansu domin yi masu wanka na al’ada. Bincike ya yi nisa kan lamarin,” in ji shi.

Su dai bokayen, ana zarginsu da yin garkuwa da mutanen ne a kokarinsu na tilasta ‘yan uwan su janye wata kara da ke gaban kotu, kamar yadda DSP ya bayyana.

Daga karshe, DSP ya ja hankali mutane da cewa, kodayake dai kowa na da ‘yancin yin duk addinin da ya aminta, to amman banda na haramtacciyar hanya ko kasuwanci kamar bokanci, in jishi, ya kuma yi kasha gak ama duk wanda su ka samu da wannan

Rahotun Leadershipayau.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN