Yadda soji da bama baman Jiragen yakin Isra'ila suka halaka Palasdinawa 140 da yara 36


Jiragen saman yaki na sojin Isra'ila na ci gaba da yin luguden wuta kan Musulmi Palastinawa a yankin Gaza. Akalla Palasdinawa 140 da yara 36 sun mutu a wannan farmakin da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa kan Palastinawa a Gaza.

Sojin Isra'ila sun kashe Palastinawa 11 yau a yankin yammacin Gaza da Isra'ila ta mamaye. 

Yanzu haka zanga zanga ta barke a yankunan Palastinawa, lamari da ya haifar da bacin rai ga dubban jama'a yayin da Isra'ila ke barazanar koran Palastinawa daga gidajensu a yankin gabacin Birnin Kudus watau Jerusalem.

Bayan kammala Salla ranar Juma'a, zanga zanga ta barke a wurare fiye da 200 a yankin, yanayi da ya yi sanadin raunata fiye da Palastinawa 500 bayan sojin Isra'ila sun yi ta auna Palastinawa masu zanga zanga suna harbinsu da bindigogi yadda suka gan dama, tare da yin amfani da harsashin gaske wajen jarbin masu zanga zanga, inji kungiyar agaji ta Red Cross a Gaza.

Dubun dubatan Palastinawa a kasar Jordan sun yi kokarin mamaye bakin iyakan kasar Jordan da Isra'ila, amma jami'an tsaron Jordan suka hanasu ranar Juma'a. Kazalika Palastinawa a kudancin kasar Lebanon sun yi kokarin kutsawa ta Bakin iyaka.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN