Yadda wani mutum ya yanke jiki ya faɗi ya mutu yayin tiƙa rawa wurin daurin aure


Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke tika rawa a wurin bikin aure a Borokiri, kusa da tsohuwar birnin Port Harcout a jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Mutumin mai suna Dein, jagoran mutane ne daga Ataba a karamar hukumar Andoni a jihar.

Lamarin ya faru a ranar Litinin yayin bikin auren dan uwansa daga Ataba wanda ya auri wata mata daga garin Asarama a karamar hukumar Andoni.

An ruwaito cewa a yayin da mutane ke zaune a wurin daurin auren, mutumin sanye da kaya masu launin fari da baki ya tashi ya fara kayatar da mutane da rawa.

Bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta a ranar Talata da Legit.ng ta gani ya nuna mutumin yana rawa kuma mutane na masa tafi kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi a kasa.

Da farko mutanen da ke zaune ba su motsa ba don suna tunanin fadin da ya yi duk cikin rawar ne inda mai jawabi wurin taron shima ya ke ba'a yana cewa watakila duk rawa ne.

Kamar yadda ya ke a bidiyon, mutumin ya yi yunkurin motsa hannunsa da kansa kamar yana kokarin tashi amma ya sake fadi kasa ya dena motsi.

Bayan yan mintuna kadan mutane sun garzaya inda ya ke a kwance domin su duba abin da ke damunsa.

Mai jawabi wurin taron wato MC ya ce, "Likita zai duba shi ya gani ko barasa ne."

An ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka hallarci taron likita ne kuma shine ya tabbatar da mutuwar mutumin.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya ce ya ga bidiyon amma a yanzu babu wanda ya shigar wa yan sanda rahoto a hukumance.

Source: Legit

Kalli bidiyo:



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN