Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal


Daya daga cikin mambobin kwamitin duba wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya, Simwal Usman Jibril, ya bayyana cewa wadanda sukayi ikirarin sun ga wata jiya kuskure suka yi.

Simwal ya yi bayanin cewa ko a yau 30 ga watan Ramadana ba zai yiwu a ga watan ba saboda wasu dalilai.

Ya bayyana hakan a shafinsa a Facebook da Tuwita.

A cewarsa, hasali ya kamata jama'a suga wata ranar 30 ga wata cikin sauki amma tunda awanni jinjirin watan bai wuce 22 ba, ba za'a gani cikin sauki ba.

Ga bayaninsa: "Hasali a ranar 30 ga watan akan ga jinjirin wata cikin sauki kuma babba. Watan na fadi ne akalla waw guda daya bayan faduwar ranar idan jinjirin wata ya bayyana a jiya."

"Amma saboda sai bayan karfe 8 na daren jiya jinjirin wata ya bayyana, Insha Allah da yamman nan awanni jinjirin watan 22 kuma zai fadi bayan mintuna 42 da faduwar rana Insha Allah amma ba za'a iya gani cikin sauki ba."

"Yanzu na gama tabbatar daga kwamitin duban wata da fadar mai martana Sarkin Musulmi cewa babu inda aka ga wata a yau a Najeriya. Ko wadanda suka ce sun gani jiya sun ce basu gani yau ba," Ya kara

"Mun bayyana karara cewa da kamar wuya a ga watan yau saboda awanni jinjirin watan 22 da yan kai. Ko wadanda suka yi ikirarin gani jiya sun gaza gani yau. Hakan na tabbatar da cewa kuskure sukayi jiya."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE