An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa


A kalla 'yan sanda hudu ne ke tsaron gidan Maikano Abdullahi, jami'in fadar shugaban kasa wanda wasu barayi suka yi yunkurin shiga gidansa.

An gano cewa jami'an tsaro biyu ke aiki a lokaci daya, rana biyu, dare biyu a gidan, jaridar The Punch ta ruwaito.

Gidan yana da kusanci da gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke da kusancin mitoci kadan da wani wurin da sojoji hudu ke zama.

Duba da aka yi an gano cewa gidan yana cikin fadar shugaban kasa ne kuma ana matukar tsaronsa domin kuwa har da maharban boye akwai.

Gidan an gano ya kasance madaddalar 'yan kwangila da ke neman kafa ta wurin Abdullahi domin samun shiga a fadar shugaban kasan akan lamurran kwangilolinsu.

Majiya daga jami'an tsaro ta ce ta yuwu barayin sun yi tsammanin ana ajiye makuden kudade a gidan ne yasa suka kai farmakin.

An gano cewa dan sanda dauke da bindiga ne ya fatattaki barayin yayin da yake kan aikinsa.

Barayin da suka tsallaka katanga ta wani layin baya sun arce bayan ganin dan sandan dake farfajiyar domin tseratar da rayukansu.

Wata majiya tace, "Abinda ya faru shine barayi sun fado ta katanga daga titin baya amma sai suka tarar da dan sanda. Hakan yasa sun sake tsallaka katangar tare da tserewa."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN