Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa


Wani fitaccen mai wa’azin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa zai je fadar Aso Rock idan ‘yan fashi suka sace dansa.

Malamin ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da BBC Pidgin wanda aka buga a ranar Juma’a, 7 ga Mayu.

Gumi ya bayyana cewa ba zai taba yin shiru ba idan yaronsa yana cikin daliban jami'ar Greenfield da aka sace.

Ya sake nanata shawarar da ya ba gwamnatin tarayya na ta biya Naira miliyan 100 kudin fansa don sakin daliban.

Malamin ya ce:

“Rayuwa da abu; haka za ku dube shi. Babban hakki ne akan gwamnati ta kare rayuka. Yanzu muna da rayukan mutane ko kuma miliyan N100 a cikin hatsari kuma rayukan matasa 17 da basu ji ba basu gani ba.

"Da ace ɗana yana wurin. Ba zan iya yin shiru ba. Zan je in kwankwasa Aso Rock, idan ɗana yana wurin. Su ma 'ya'yana ne."

Ya ce ‘yan fashi ba sa jin zafin satar mutane saboda ba su da ingantaccen ilimi.

Gumi ya ce ya sanar da gwamnati cewa idan ‘yan fashi suna da makarantu, ba za su afkawa mutane ba.

A gefe guda, fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci tsarin shari’a nan ba da jimawa ba kasancewar gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da su.

Babban Atoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana wannan ci gaban a ranar Juma'a, 7 ga watan Mayu, jaridar Punch ta ruwaito.

Malami wanda bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba ko kuma yawan mutanen da abin ya shafa ba ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, in ji jaridar The Cable.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN