Kano: Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Kwankwasiyya


Hargitsin cikin gida ya fara tsakanin mabiyan kungiyar Kwankwasiyya dake jihar Kano. Hakan ta faru ne sakamakon rabon kayan abinci na azumi na miliyoyin naira da wani yayi wa 'yan jam'iyyar a Kano.

Hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanusi Surajo, ya sanar da cewa ya ga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda Dakta Adamu Dangwani ke shirin farraka kan 'yan Kwankwasiyyan.

Dangwani tsohon kwamishinan ruwa ne kuma shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano yayin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A zargin da ake masa, akwai na kalubalantar Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida saboda bai samu damar takara ba a 2019.

Kamar yadda Sanusi Surajo ya sanar, "Babu dan takarar gwamnan da za mu yi na'am da shi ban da Abba Gida Gida, hakan yasa zamu yi watsi da duk wani kira na daban, don haka Dangwani yayi watsi da kudirinsa ko kuma ya bar tafiyarmu.

"Hatta Kwankwaso ba zai sauya mana Abba ba, idan baka bayan Abba, toh abu mafi sauki shine ka fice da tsarin ko ka bar jam'iyyar baki daya.

"Abba ya samu karbuwa kuma ba za mu canza shi ba. Muna sane da irin zagon kasa da ake yi wa Sanata Kwankwaso kuma ba wanda zai ci galaba da izinin Allah."

Dangwani ya fara suna ne bayan rabon kayan azumi da yayi ga 'yan Kwankwasiyya. Yanzu haka dai yana samun magoya baya daga shugabanni da mambobin Kwankwasiyya kuma suna kira garesa da ya fito takarar Gwamnan jihar.

Har a halin yanzu, ba a ji uffan daga bangaren Dangwani ba kan zargin da ake masa.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN