Fitaccen Malamin addinin Musulunci kuma shugaba a Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da nadin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a matsayin Khalifan Tijjaniyya tare da yi masa fatan alhairi.
Sheikh ya furta kalaman amincewa da sabon mukamin na Sanusi ne ranar Litinin lokacin da Sanusi ya gabatar wa Sheikh takardar nadin nasa a zaman Khalifan Tijjaniyya na Najeriya a gidansa da ke Birnin Bauchi. Daily trust ta ruwaito.
Sheikh ya ce nadin Sanusi ba wai yana nufin ya rage karfin tasirin shugabannin Tijjaniyya bane, musamman musamman wadanda Maulana Sheikh Ibrahim Nyass ya nada da kanshi.
Dahiru Bauchi ya ce "Nadin ka a matsayin Khalifan Tijjaniyya kamar Janar ne a cikin soji, ko a cikin Janar akwai manya. Muna yi maka maraba a matsayin Khalifan Tijjaniyya. Muna kuma martaba basirarka tare da hangen nesa da girmama shugabanni. Ina bukatar ka yi koyi da Kakanka Muhammad Sanusi na 1".
" Na yi murna da farin ciki na nadi da aka yi maka a matsayin shugaba, kuma Ina fatar Allah ya jagorance ka ya kuma kiyaye ka a wannan mukami".
Shehin Malamin ya bukaci kada Sanusi ya bari abokan sa su yi masa katsalandan a harkar jagorancin sabon mukaminsa. Ya ce wannan harkar addini ne da bai kamata a cudanya shi da harkokin kasuwanci ko siyasa ba.
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari