Bill Gates ya yi murabus daga kamfanin Microsoft saboda zargin alaka da ma'aikaciyarsa


A shekarar da ta gabata lokacin da Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft, ya ce aikin agaji ne ya sa ya yanke shawarar, amma sabon rahoto na danganta ficewar tashi da wani lamari da ya faru kusan shekaru 20 da suka gabata.

An ce yana karkashin bincike game da lamarin a shekarar 2019, yayin da kwamitin Microsoft ya nemi Gates ya sauka daga shugabancin kamfanin yayin da binciken ke gudana.

Maganar da ake zarginsa dashi ta kasance tare da wata injiniyar kamfanin Microsoft da ba a bayyana sunanta ba, wacce ta bayyana alakarta da shi a wata wasika. Lamarin ya bayyana ne yayin da Gates da matarsa, Melinda, ke fuskantar cuku-cukun saki.

Daraktocin ba su ga dacewar ya kasance a shugabancin kamfanin ba a shekarar 2020 yayin da binciken ya kare, wanda kuma shi ne shekarar da Gates ya yi murabus don fuskantar ayyukan agaji.

Amma wata mai magana da yawunsa ta ce attajirin bai yi murabus saboda binciken ba, in ji Reuters.

Ba a bayyana dalilin binciken ba, amma an bayar da rahoton lamarin cikin aminci.

An ruwaito cewa matan da ke aiki a Microsoft da Gidauniyar Bill da Melinda Gates kan sami alheri daga Bill Gates a wasu lokuta. Har yanzu yana kula da gidauniyar.

Ku lura cewa Gates ya bar shugabancin Microsoft kafin a kammala binciken. Sakamakon binciken wanda wata hukumar dokoki ta gudanar ba a sanar da shi ba.

A wani labarin, Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Ma'auratan sun dade suna jagorantar ayyuka da dama na taimakon jama'a a sassan kasashen duniya daban-daban.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN