Sadiq Khan, musulmi na farko da ya taɓa riƙe muƙamin magajin garin Landan ya sake komawa kujerarsa a karo na biyu..
Rahoton BBC ya bayyana cewa Sadiq Khan ya sake komawa kan kujerar sa ne bayan doke abokin takararsa, Shaun Bailey, na jam'iyyar Conservative.
Khan ya samu nasara da kashi 55.2% yayin da ya kayar da abokin takarar sa Baily wanda ya samu 44.8% a zagaye na biyu na zaɓen da aka gudanar.
Sadiq Khan wanda tsohon dan majalisa ne, shine musulmi na farko da ya fara lashe zaɓen magajin garin Landan a shekarar 2016, ya kuma sake komawa kujerarsa a karo na biyu.
Khan yace: "Nayi matuƙar farin ciki da irin amincewar da mutanen Landan suka mun na in sake jagorantar birnin da yafi kowanne a faɗin ƙasa."
"Na yi alƙawarin zan yi amfani da kowacce irin dama da nike da ita wajen kawo kyakkyawan cigaba a Landan bayan wannan annobar da muke fama da ita ta shuɗe."
Source: Legit Nigeria
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari