Kebbi: Abubakar Malami ya taba rayuwar talakawan jihar Kebbi da wani abin alhairi, mai shekara 80 ya yi hawayen farin ciki


Ministan Sharia kuma babban Atoni janar na Najeriya Abubakar Malami ya gwangwaje talakawan jihar Kebbi da kyautar kayan masarufi har da buhuhuwan shinkafa akalla buhu biyu zuwa uku a kowane gida, wanda gidaje guda 10.000 a fadin jihar Kebbi suka samu.

Alherin ya isa gidajen talakawa bisa umarnin Abubakar Malami, an bayar da fifiko ga Marayu, Nakasassu, Matalauta da sauran marasa karfi a jihar Kebbi.


Lamari da ya sa wani tsoho mai shekara 80 da baya son mu ambaci sunansa ko unguwar da yake zaune, ya fashe da kukan farin ciki bayan ba zato ba tsammani ya sami buhun shinkafa guda 3 a gidansa lokacin rabon kayan masarufi da kungiyar Khadimiyya ta Abubakar Malami ta bayar a watan Ramadan.

An gudanar da rabon kayan masarufi ne a fadin jihar Kebbi har da kananan hukumomi. 


Masana harkokin siyasar jihar Kebbi sun yi hasashen cewa taimako da Malami ya bayar ga talakawan jihar Kebbi a watan Ramadan,  ya zarce wanda wasu yan siyasa suka ba jama'arsu.

Duba da cewa idan bancin Gwamnatin jihar Kebbi, babu kyautar dan siyasa da ta hade gabadayan jihar Kebbi sai kyautar da Abubakar Malami ya bayar wanda ya sami kyakkyawan tsarin tafiyarwa daga kungiyarsa ta Khadimiyya.


Malami ya assasa kungiyar Khadimiyya for justice and development initiative ne domin taimakon talakawa tare da ceton al'umma. Ta wannan kungiyar kuma ake tafiyar da harkokin jinkai ga al'umma.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN